fidelitybank

Zulum ya ziyarci sansanin ‘yan gudun hijira da gobara ta kama

Date:

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ziyarci sansanin ‘yan gudun hijira na Muna Elbadawy da ya kama da gobara a jihar.

Zulum ya umarci hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Borno (SEMA) da ta lissafa tare da mika bayanai kan adadin gidajen da gobara ya shafa ,domin gwamnatin jihar ta tallafa musu.

Zulum ya kai ziyarar ne a ranar Asabar, 19 ga watan Fabrairu, inda ya zagaya wajen da annobar ta afku.

Gobarar wacce ta tashi a sansanin ‘yan gudun hijirar da ke wajen Maiduguri, ta hallaka rai daya, sannan ta jikkata mutane 17, yayin da ta lalata matsuguni sama da guda 100.

Sansanin na dauke da gidaje fiye da 10,000 da mutane 50,000 ke zaune.

Gwamnan ya kuma sanar da cewar, gwamnatin jihar na duba yiwuwar hada hannu da gwamnatin tarayya da hukumomin agaji, domin mayar da su da sauran ‘yan gudun hijira da ke Maiduguri da kewaye, zuwa gidajensu ko garuruwa mafi kusa irin su Ngwom da sauransu.

nnn

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp