fidelitybank

Zulum ya ware gidaje 259 da Naira miliyan 110 ga ƴan sanda

Date:

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, a ranar Alhamis a Maiduguri, ya bayyana cewa, gwamnati ta ware gidaje 259 tare da sakin Naira miliyan 110 ga rundunar ‘yan sandan Najeriya a jihar.

Zulum ya bayyana hakan ne a lokacin kaddamar da bankin ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Borno (NPFM Bank).

An tsara bankin Microfinance ne don samar da ayyukan kudi don tallafa wa kanana da matsakaitan sana’o’i ga iyalan ‘yan sanda, ‘yan uwansu da fararen hula a jihar Borno.

Bude bankin a Maiduguri ya samu halartar babban sufeton ‘yan sanda, Usman Baba Alkali.

Na farko, in ji Zulum, an yi amfani da Naira miliyan 25 don raba wa iyalan ‘yan sandan da suka mutu a bakin aiki.

Ya ba da umarnin a ajiye kudaden a asusun ajiyar yaran da jami’an ‘yan sandan da suka mutu suka bari a baya.

Kudaden Naira miliyan 30, inji gwamnan, za a saka shi a asusun ajiyar kudi, domin tallafa wa matan ‘yan sanda da ke aiki a fadin jihar Borno.

Zulum ya yabawa IGP Alkali, bisa kaddamar da reshen bankin na Borno wanda ya ce, ya nuna yadda IGP ya ba da fifiko ga jin dadin ‘yan sanda.

spw news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp