fidelitybank

Zulum ya umarci da a duba mutanen da ‘yan Boko Haram suka jikkata kyauta

Date:

Mutum takwas sun sun mutu yayin da wasu da dama suka jikkata bayan da wata motar bas ta taka nakiya a kan hanyar Maiduguri zuwa Damboa a ranar Asabar.

Gwamnan jihar Babagana Umara Zulum ya zargi ƙungiyar Boko Haram da dasa nakiyar a kan babban titi da ya haɗa Maiduguri, babban birnin jihar da kuma garin Damboa.

A baya rundunar sojin Najeriya ta rufe titin sakamakon ta’azzarar matsalolin tsaro a yankin.

Daga baya ne gwamnan jihar ya bayar da umarnin buɗe titin inda sojoji ke bai wa matafiya kariya ta hanyar yi musu rakiya.

To sai dai gwamnan ya ce harin na jiya Asabar ba zai sa a daina bin titin ba.

“Za mu tabbatar da cewa an ci gaba da zirga-zirga tsakanin Maiduguri zuwa Damboa, wannan hari ba zai hana mu bin titin ba,” in ji Gwamna Zulum.

Dasa nakiyoyi ya kasance ɗaya daga cikin hanyoyin da ƙungiyar Boko Haram ke kai hare-hare. Ko a shekarar da ga gabata ma irin wannan hari ya kashe sojojin ƙasar bakwai, bayan da motarsu ta taka nakiya.

A baya-bayan nan dai hare-haren Boko Haram na sake dawowa musamman a jihar Borno, lamarin da ya sa gwamnan jihar ya fito ya koka a baya-bayan nan.

www.legitnews.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp