Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya amince da rusa majalisar zartarwa ta jihar.
Sakataren gwamnatin jihar, Usman Shuwa, ya sanar da rusa majalisar gwamnan ranar Alhamis, yana mai cewa hakan ya fara aiki nan take.
Sanarwar hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren ma’aikatar mulki da ma’aikata, Danjuma Ali, kuma aka rabawa manema labarai a Maiduguri, babban birnin jihar.
Gwamna Zulum, a cewar sanarwar, ya umarci dukkan wadanda abin ya shafa da su mika ragamar shugabancin ga sakatarorin dindindin a ma’aikatun su.
Ya bayyana cewa, rusasshiyar ta yi ne domin a samar da yanayi mai kyau ga ‘yan majalisar masu sha’awar shiga takara a jam’iyyar ta APC a bisa doka.
Zulum ya godewa ’yan majalisar zartarwa bisa irin gudunmawar da suka bayar a lokacin da suke rike da mukamai tare da yi musu fatan alheri a kan ayyukansu na gaba.