fidelitybank

Zulum ya rabawa ƴan gudun hijira gidaje 893

Date:

Gwamna jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ƙaddamar da sabbin rukunin gidaje da gwamnatinsa ta gina wa ‘yan gudun hijira a Ƙaramar Hukumar Konduga ranar Laraba.

A cewar gwamnatin jihar, an sake gina gida 803 ne, bayan shekara bakwai suna gudun hijira, sakamakon hare-haren mayaƙan ƙungiyar Boko Haram.

Wata sanarwa da Isa Gusau, mai magana da yawun gwamnatin Borno, ya fitar ta ce, Zulum ya ba da umarnin a bai wa mutum 500 Naira 100,000 kowannensu waɗanda gidajensu ba sa cikin waɗanda aka sake ginawa, inda za a raba musu miliyan 50 jumilla.

Kazalika, gwamnan ya ba da umarnin raba wa maza 240 ‘yan gudun hijirar da suka koma garinsu naira N200,000 kowannensu. Sannan kowace mace daga cikin 379 za ta samu N10,000 da kuma atamfa.

Sanarwar ta ƙara da cewa, gwamnan ya yaba wa hukumar ci gaban yankin Arewa maso Gabas ta North-East Development Commission (NEDC), bisa taimakon kayan abinci da take baiwa ‘yan gudun hijirar.

legit news.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp