fidelitybank

Zulum ya nuna ɓacin ransa a kan halin asibitin Gwoza ke ciki

Date:

Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum, ya nuna damuwarsa kan rashin wutar lantarki da sauran yanayin da ya samu babban asibitin garin Gwoza.

Gwamnan ya bayyana ɓacin ransa a lokacin da ya kai wa asibitin ziyarar ba-zata da tsakar daren ranar Asabar.

Cikin wata sanarwa da gwamnan ya wallafa shafinsa na Twitter, ya ce ya kwana a garin wanda shi ne shalkwatar karamar hukumar Gwoza da ke kudancin jihar.

A ziyarar Zulum ya kewaya sassan asibitin domin duba irin kayayyaki da yadda asibitin ke aiki.

A lokacin ziyarar gwamnan ya nuna damuwarsa kan yadda ya samu asibitin.

Ya ce ”Abin takaici ne halin da babban asibitin garin Gwoza ke ciki, babu manyan abubuwan buƙata a asibitin kamar wutar lantarki. Hakiƙa hakan zai kawo cikas da cutarwa ga marasa lafiyar da ke kwance a asibitin, tare da durƙusar da shirinmu na inganta asibitoncin jiharmu”.

Gwamnan ya kuma nuna ɓacin ransa kan rashin sanar da shi halin da asibitin ke ciki.

”Ba zan iya wanke kai na ko ƙaramar hukuma daga wannan laifi ba, dukanmu mun gaza samar da abin da ake buƙata”.

Zulum ya kuma tabbatar wa da marasa lafiyar da ke kwance a asibitin cewa, za a magance matsalolin da asibitin ke fuskanta, inda nan take ya bayar da umarnin fara gyara wuraren da suka lalace ciki har da wutar lantarkin asibitin.

Haka kuma gwamnan ya yaba wa ma’aikatan asibitin, waɗanda duk da rashin hali mai kyau da asibitin ke ciki ya same su a bakin aikinsu, inda ya alƙawarta saka mu su da alkairi kan sadaukarwar da ya ce suna yi duk kuwa da tarin kalubalen da suke fuskanta.

Gwamna Zulum ya saba kai irin wannan ziyara ta ba-zata zuwa makarantu da asibitoci a fadin jihar, a wani yunƙurin na sanin haƙiƙanin halin da suke ciki. In ji BBC.

benue news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp