Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya amince da nadin Alhaji Dauda Iliya a matsayin mai magana da yawunsa kuma mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai.
Nadin ya biyo bayan rasuwar Mallam Isa Gusau wanda har ya rasu a watan Fabrairun 2024 a matsayin mai magana da yawun gwamnan.
Sanarwar amincewar gwamnan ta fito ne a wata sanarwa a ranar Juma’a ta hannun SSA a Sabbin Kafafen Sadarwa, Abdurrahman Ahmed Bundi.
Dauda Iliya a halin yanzu shi ne shugaban kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya reshen jihar Borno.
Ya fito daga karamar hukumar Kwaya-Kusar da ke kudancin jihar Borno.
Ya yi digirinsa na farko a fannin nazarin harsunan Ingilishi daga Jami’ar Maiduguri, sannan ya samu digirinsa na biyu a Mass Communications daga wannan jami’ar a shekarar 2024. Ya halarci kwasa-kwasai da dama da kuma horarwa.
Sabon wanda aka nada memba ne na kwararru da dama da suka hada da kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya da kungiyar masu yada labarai ta Najeriya.