fidelitybank

Zulum ya lashe zaɓen fidda gwani da ƙuri’a 1,411

Date:

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya lashe zaben fidda gwanin jihar da aka yi, ya kuma yi watsin da masu yi masa ta yin ya nemi mataimakin shugaban ƙasa.

Babagana wanda shi kadai ne dan takarar a karkashin jam’iyyar APC ya lashe zaben ba tare da hamayya ba, wanda hakan zai ba shi damar karawa da takwarorinsa na sauran jam’iyyun a zaben 2023.

An yi zaben fidda gwanin ne a cibiyar wasanni ta El-Kanemi da ke Maiduguri a yammacin Alhamis, kuma manyan ‘yan jam’iyyar APC sun halarci zaman ciki har da tsofaffin gwamnonin jihar da suka hada da Kashim Shettima da Ali Modu Sheriff da kuma Maina Ma’aji Lawan.

Ministan noma Mustapha Baba Shehuri da tsohon dan majalisar dattijai kuma Ambasadan Najeriya a China Baba Ahmed Jidda duk suna cikin mahalarta taron.

Uba Maigari Ahmadu wanda shi ne shugaban zaben fidda gwanin gwamnonin da na ‘yan majalisa jihar Bornon ya sanar da cewa Zulum ya lashe zaben ne da kuria 1,411.

daily sun news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Majalisa ta gayyaci Gwamnan Filato kan tsaron jihar

Kwamitin wucin gadi kan matsalolin tsaron jihar Filato na...

Sojoji sun sun kashe ‘yan Boko Haram 24

Rundunar Sojoji ƙarƙashin rundunar 'Operation Hadin Kai' mai yaƙi...

Dangote zai gina rumbum man fetur da dizel a Namibia

Matatar mai ta Dangote da ke Najeriya za ta...

Dangote ya rage farashin litar mai zuwa ₦820

Kamfanin matatar man Dangote ya rage farashin litar mai...

Dubai ta sake tsaurara matakan bai wa ‘yan Najeriya biza

Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, UAE ta sake sanya wasu dokoki...

‘Yan Bindigar Katsina ‘yan asalin jihar mu ne – Gwamna

Gwamnan Katsina Umaru Dikko Radda ya ce galibin 'yan...

Zan yi wa ADC aiki ina cikin jam’iyyar PDP – Sule Lamido

Jigo a babbar jam’iyyar hamayya ta PDP a Najeriya...

Buhari da Tinubu kan su a hade ya ke – Garba Shehu

Mai magana da yawun tsohon Shugaban kasa, Muhammadu Buhari...

Ganduje ya kama aiki a hukumar kula da filayen jirgin sama

Tsohon shugaban jam'iyyar APC mai mulki, Abdullahi Ganduje, ya...

JAMB ta amince da maki 150 mafi ƙanƙanta don samun gurbin karatu a jami’o’i

Hukumar shirya jarrabawar shiga Jami'o'i ta Najeriya (JAMB) ta...

ASUU ta dakatar da yajin aikin da ta fara

Ƙungiyar Malaman Jami'o'i ta Najeriya, ASUU da dakatar yajin...

Masu haɗakar ADC na ɓaɓatu ne saboda rashin gwamnati – Radda

Gwamnan jihar Katsina, Mallam Dikko Umar Radda ya yi...
X whatsapp