Gwamantin jihar Borno tare da hadin gwiwar hukumar raya kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya, sun kaddamar da bude gidaje 804 wadanda suka sake ginawa domin tsugunar da al’umomin Ngarannam a jihar.
Shugaban ma’aikatar fadar shugaban Najeriya Farfesa Ibrahim Gambari ne ya kaddamar da bude gine-ginen.
Gwamna Zulum ya mika wa al’umomin gine-gine 360 da suka hadar da shaguna, da makarantu, da gidaje ga malaman makaranta, da jami’an tsaro tare da ginin ofishin ‘yan sanda daya.
Gwamnan jihar ya fada a cikin wata sanarwa cewa daga cikin gidajen 804, a yanzu an kammala 564.
Ya kara da cewa gwamnatin jihar za ta gina gida 304, a yayin da hukumar ta UNDP za ta gina gida 500.
Haka kuma sanarwar ta ci gaba da cewa sun bayar da kyautar shanu 2,674, da tufafi da abinci da kyautar kudi naira 100,000 ga duk magidanci