Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya gwangwaje jami’an tsaro da motocin sintiri, domin ci gaba da bayar da tsaro a jihar.
A cewar wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar, gwamnan na Borno, ya ba da kyautar motocin sintirin ne, domin karfafawa gwiwa ga sojoji da ‘yan sa kai da mafarauta da ’yan banga da suka sadaukar da kai ga sintiri a hanyar Maiduguri da Dikwa da kuma Gamboru.
Zulum ya mika kyautar motocin ne ga kwamandan Operation Hadin Kai, wanda rundunar soji ta ji dadin wannan kyauta, wadda ta tabbatar da goyon baya da ci gaba da aiki tukuru wajen wanzar da zaman lafiya.
Yankuna da dama na fama da rashin tsaro a jihar Borno, musamman ganin yadda ‘yan ta’addan Boko Haram da ISWAP ke addabar yankin Arewa maso Gabas.
Zulum ya mika motocin ga kwamandan Operation Hadin Kai, Manjo Janar Christopher Musa, yayin da ya ke kaddamar da shirin bude hanyar tattalin arziki ga matafiya a ranar Juma’a.