Gwamnatin jihar Borno ta ƙaddamar da wani tsarin karatu ga dubban yaran da rikicin Boko Haram ya ɗaiɗaita.
Gwamnan jihar Babagana Zulum ne ya ƙaddamar da tsarin a garin Monguno inda waɗanda rikicin ya shafa suke samun mafaka a sansanoni bayan da suka rasa muhallansu.
An yi wa wasu yara 7,000 rajista a makarantun Firamare da ƙaramar sakandare a kashin farko na shirin kamar yadda kakakin gwamnan ya shaida wa BBC.
Hukumomi sun ce galibin waɗanda suka ci gajiya yara ne da rikicin ya mayar da su marayu. Sun ce shirin na da burin shigar da fiye da yara 200,000 makarantun da ke jihar.
Rikicin na Boko Haram wanda aka fara a 2009, ya halaka dubban mutane tare da ɗaiɗaita miliyoyi a yankin arewa maso gabashin ƙasar da kuma wasu ƙasashe maƙwabta.
Tashin hankalinya tilastawa yara daina zuwa makaranta, wasu kuma ba sa ma iya shiga makarantar. An kuma lalata makarantu da dama.
Hukumomi sun ce suna ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da yara sun koma makaranta ta hanyar gina sabbin makarantu da kuma basu tallafin karatu.


