Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno, ya kara wa malaman jihar wa’adin ritaya da shekaru biyar.
Hakan na kunshe ne a wata takardar da ta fito daga hukumar kula da aikin koyarwa ta jihar Borno mai dauke da sa hannun babban sakataren dindindin, Malam Yusuf Garga.
“Hankalin daukacin malamai yana nan kan yadda Gwamna Babagana Zulum, ya amince da tsawaita wa’adin hidimar duk malaman Borno daga shekaru 35 zuwa 40 sannan daga shekara 60 zuwa 65 duk wanda ya zo na farko.
“Dukkan malaman da ke da sha’awar jin daɗin hakan ana sa ran su rubuta wa hukumar ta hannun shuwagabannin su suna nuna sha’awarsu tare da haɗa takardar shaidar lafiyar jiki daga kowane asibitin gwamnati,” in ji sanarwar.
Irin waɗannan wasiƙun, in ji shi, za a gabatar da su ga hukumar da kai tsaye