Jirgin kasa mai sulke dauke da shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un, ya shiga Rasha, a hanyar ganawa da shugaba Putin.
Koriya ta Kudu da Japan sun ba da rahoton cewa jirgin Mista Kim ya isa garin Khasan da ke gabashin kasar, kuma tuni ya doshi Vladi-vostock.
Wannan shi ne karo na farko da Mista Kim ke fita zuwa wata kasa a cikin shekaru hudu.
Amurka ta nuna matukar damuwarta kan yiwuwar Koriyar ta sayar wa Rasha makaman yakar Ukraine.
Sannan ana zargi Mista Kim zai nemi taimakon Rasha a fannin abinci da kudade da fasahar kirkirar makamai.


