Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, zai halarci taron zaman lafiya a birnin Paris na kasar Faransa, wanda aka shirya gudanarwa a ranar 11 ga watan Maris.
Muhammadu Buhari, ya bar fadarsa ta Aso Villa ranar 26 ga watan Fabrairu, 2022, wanda zai tattaunawa da shugabannin duniya kan abin da ya shafi zaman lafiya, tattalin arziki da lamarin Korona.
A rahoton da TVC News ta fitar ta ce, jirgin shugaba Buhari ya ɗira a filin sauka da tashin jiragen sama na Le Bourget da misalin ƙarfe 7:45 na daren ranar Asabar. A cikin ziyarar mako biyu, a na tsammanin shugaban ƙasan ya halarci taron zaman lafiya na kwana uku da aka shirya gudanarwa daga ranar Jumu’a 11 ga watan Maris, zuwa Lahadi 13 ga watan Maris.