Babban kwamandan sojin sama na Zimbabwe, Air Marshal Elson Moyo, ya bayyana buƙatar ƙasarsa na neman tallafin dabarun aiki daga rundunar sojin saman Najeriya.
Moyo ya bayyana buƙatar ne a lokacin da ya ziyarci babban hafsan sojin saman Najeriya Air Marshal Oladayo Amao, a shalkwatar rundunar sojin saman Najeriya da ke Abuja babban birnin ƙasar.
Daraktan sashen hulda da jama’a da yaɗa labarai na rundunar Air Commodore Ayodele Famuyiwa, ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.
Babban kwamandan sojin saman Zimbabwe ya buƙaci tallafin rundunar sojin saman Najeriyar a ɓangarorin da suka shafi bincike da ci gaba, da fannin fasahar jiragen yaƙi da gudanarwa da yadda za a yi aiki da jiragen yaƙin ƙirar F7 da Mi-35.
Moyo ya ce ɓangarorin da ƙasarsa ke neman taimakon Najeriyar, ɓangarori ne da rundunonin sojin saman ƙasashen biyu duka ke amfani da su, musamman jiragen yaƙin da ƙasashen biyu ke amfani da su.
Ya ce a cikin ɗan takaitaccen lokaci rundunar sojin saman Najeriya ta samu gagarumin ci gaba wajen gina kanta da amfani da dabarun cikin gida.
A yayin da yake jawabi a nasa ɓangaren, babban hafsan sojin sama na Najeriya Air Marshal Oladayo Amao, ya ce rundunar a shirye take domin ƙulla ƙawancen da zai amfanar da juna tsakaninta da takwararta ta Zimbabwe.
Amao ya ce, a yanzu haka rundunar sojin saman Najeriya ta ƙulla ƙawance da ƙasashe da dama a nahiyar Afirka da ma wajenta, yana mai cewa a kodayaUshe rundunar a shirye take domin taimaka wa ƙasashen da ke buƙatar taimakonta.
Ya ƙara da cewa haɗin kai tsakanin rundunonin sojin ƙasashen Afirka zai taimaka wajen magance matsalolin tsaron da nahiyar ke fuskanta