Gwamnatin Zimbabwe ta amince da wani kudirin doka da zai soke hukuncin kisa a ƙasar.
Matakin na zuwa ne kusan shekaru 20 bayan da kasar ta aiwatar da hukuncin kisa na karshe.
Majalisar zartaswar ƙasar dai ta goyi bayan kudurin dokar da za ta kawo ƙarshen hukuncin kisa.
Ministan yaɗa labaran kasar Jenfan Muswere a ranar Talata ya ce majalisar ministocin ta yanke shawarar ne bayan da gwamnatin ƙasar ta amince da kudirin doka.
Majalisar ministocin kasar Ta ba da shawarar maye gurbin hukuncin kisa da daurin rai da rai a matsayin mafi girman hukunci a ƙasar. A cewar BBC.
A baya dai, shugaban ƙasar, Emmerson Mnangagwa ya soki hukuncin kisa.
An taɓa yanke masa hukuncin kisa a shekara ta 1965 bayan zargin da aka yi masa na tayar da bam a cikin jirgin kasa a lokacin da yake yaƙi da ‘yan tsiraru fararen fata.
Sai daga baya kuma aka sassauta hukuncin kisan na Mista Mnangagwa bayan lauyoyinsa sun yi zargin cewa bai kai shekaru ba, bisa doka, maza masu shekaru tsakanin 21-70 ne kawai za a iya kashe su.
Hukuncin kisa na Zimbabwe ragowa ne na dokar zamanin mulkin mallaka. Tun shekarar 2005, ƙasar ba ta aiwatar da hukuncin kisa ba.