Shugaba Volodymyr Zelensky na kasar Ukraine, ya kai ziyarar ba-zata a taron ƙasashen Larabawa wanda ke gudana a Saudiyya
Hakan na zuwa ne kafin batun tafiyarsa zuwa Japan inda ƙasashe Masu Karfin Tattalin Arziki suke gudanar da babban taronsu.
Wannan na cikin yunƙurin Ukraine na neman goyon bayanta daga ƙasashe musamman waɗanda ke ƙawance da Rasha.
Cikin Kungiyar Kasashen Larabawa Syria ce kawai ta fito fili ta nuna goyon bayanta ga mamayar Rasha, kuma wannan ne lokaci da na farko da Shugaba Bashar al-Assad ke halarar taron tun bayan da aka kori Syria daga kungiyar shekaru 12 da suka gabata.
Ƙarfin ikon da Saudiyya ke da shi a gabas ta tsakiya ya yi tasiri a mamayen da Rasha ke yi a Ukraine.
Saudiyya dai ta soki matakin ƙasashen yamma na ƙaƙaba wa Rasha takunkumi duk da cewa tana ɗasawa da ƙasashen.