Gwamnan jihar Ondo kuma ɗan takarar jam’iyyar APC mai mulkin jihar, Lucky Aiyedatiwa ya kaɗa ƙuri’arsa a zaɓen.
Mista Aiyedatiwa ya kaɗa ƙuri’arsa na rumfar zabensa da ke yankin ƙaramar hukumar Ilaje.
A watan Disamban bara ne aka rantsar da Aiyedatiwa a matsayin gwamnan jihar bayan rasuwar tsohon gwamna marigayi Rotimi Akeredolu.