fidelitybank

Zaɓen Najeriya ya gaza cimma yadda ‘yan ƙasar suka yi tsammani – Amurka

Date:

Sama da mako guda bayan gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya, Amurka ta ce, zaɓen ya ya gaza cimma yadda ‘yan ƙasar suka yi tsammani.

Hukumar zaɓen ƙasar ta ayyana Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC a matsayin wadda ya lashe zaɓen da adadin ƙuri’u 8,794,726, tazarar ƙuri’a kusan miliyan biyu tsakaninsa da Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP.

Atiku mai shekara 76, ya samu ƙuri’a 6,984,520, yayin da Peter Obi na LP – wanda a ƙasa da shekara guda ya tara matasan mabiya- ya bayar da mamaki a takarar inda ya samu ƙuri’a 6,101,533.

To sai dai Atiku da Obi dukkansu sun yi zargin maguɗi a zaɓen, inda suka sha alwashin ƙalubalantar nasarar Tinubu a kotu.

A wata sanarwa da Amurkan da fitar ta hannun jakadiyar ƙasar a Najeriya Mary Beth Leonard, ta ce ‘yan Najeriya da dama sun fusata game da sakamakon, inda wasu suka riƙa murna kan nasarar da suka samu.

Sanarwar ta ƙara da cewa “A bayyane take cewa tsarin zaɓen Najeriya da aka gudanarar ranar 25 ga watan Fabrairu ya gaza cimma yadda ‘yan ƙasar suka yi tsammani,”

“Kamar yadda na sha faɗa a baya gabanin zaɓen, Najeriya ta cimma abubuwa masu yawa a tsawon shekaru sama da 20 da ta yi bayan komawa tafarkin dimoraɗiyya, kuma ci gaban da aka samu a fannin zaɓukan ƙasar na daga cikin nasarorin da ƙasar ta cimma”

“Yan Najeriya sun nuna sadaukarwarsu ga dimokraɗiyya ranar 25 ga watan fabrairu, to sai dai da yawa sun nuna fusata, yayin da wasu da dama suka nuna murna bayan nasarar da suka samu”. In ji BBC.

nnn.ng

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp