A wani yunkuri na haɗa kan jam’iyyar PDP gabanin zaben 2023, Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue a ranar Talata, 17 ga watan Mayu, 2022 ya ziyarci tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan a gidansa na Maitama da ke Abuja.
Gwamna Ortom ya taba rike mukamin karamin ministan kasuwanci da zuba jari sannan kuma ya zama ministan sufurin jiragen sama a lokacin Jonathan.
Mutanen biyu sun hadu bayan sun rufe kofa sama da mintuna 40.
Duk da cewa babu daya daga cikinsu da ya yi magana da manema labarai a lokacin da suka fito, suna ta murmushi tare da tsohon shugaban kasar suna musabaha da kowa da kowa a cikin tawagar Gwamnan.