Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) a ranar Juma’a ta ce, ta tura jami’an tsaro dari biyu da ke yaki da sayen kuri’u a jihohin Kano, Jigawa da Katsina a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya da za a yi ranar Asabar.
Kwamandan hukumar EFCC na shiyyar Kano Farouk Dogondaji ne ya bayyana haka yayin wata tattaunawa da NAN a Kano.
Dogondaji ya ce tura sojojin wani bangare ne na kudirin EFCC na tabbatar da sahihin zabe na 2023 a shiyyar.
Ya ce, “Mun tura jami’ai 50 domin sanya ido kan yadda zaben ke gudana a jihar Kano, hamsin a jihar Jigawa, hamsin kuma a jihar Katsina domin hana sayen kuri’u a duk lokacin gudanar da zabe.
“Sauran jami’ai [hamsin] an tura su zuwa filin jirgin saman Malam Aminu Kano da ke Kano da kuma filin jirgin Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina.”
A cewar Dogondaji, hukumar na da isassun jami’an tsaro, inda ya kara da cewa a shirye suke don fuskantar duk wata barazana ko da a lokacin zabe da kuma bayan zaben.
A yau Asabar ne za a gudanar da babban zaben shekarar 2023 a fadin Jihohin Najeriya 36 ciki har da babban birnin tarayya.