fidelitybank

Zargin ƙazafi: Gwamna Masari ya nemi ƴan jaridar Abuja su biya shi diyyar N10bn 

Date:

Gwamna Aminu Bello Masari na Jihar Katsina ya bukaci Ƙungiyar ƴan Jarida ta Ƙasa, NUJ, reshen Abuja da ta biya shi diyyar Naira biliyan 10 biyo bayan wata sanarwar manema labarai da su ka fitar, inda ya ke zargin sun ɓata masa suna.
Masari ya kuma buƙaci ‘yan jaridun da su bayar da haƙuri a hukumance a jaridun ƙasa guda takwas nan da kwanaki bakwai masu zuwa ko kuma su fuskanci hukuncin Shari’a.
Da yake zantawa da manema labarai a Katsina, a ranar Alhamis, Lauyan Masari,  E.O. Obunadike, ya ce wanda ya ke karewa ya yanke shawarar daukar irin wannan matakin ne domin kare mutuncinsa da ya gina shi ashekaru da dama.
Idan dai ba a manta ba, ‘yan jaridan biyu Emmanuel Ogbeche da Ochaika Ugwu, shugaba da sakataren  NUJ ne su ka fitar da wata sanarwa a ranar 2 ga watan Janairu, inda su ke zargin Masari ya bayar da umarnin kama Nelson Omonu na jaridar Summit Post a Abuja.
Sun yi zargin cewa gwamnan ya bayar da umarnin kama Nelson a Katsina bayan ya zarge su da ɓata masa suna.
Sai dai kuma da ga bisani Ugwu da Ogbeche sun fitar da wata sanarwa inda suka nemi gafarar Gwamna Masari, saboda sun zaci ya bada umarnin kama shi.
Amma Obunadike, ya ce haƙurin nasu bai isa ba, don haka ya ce ‘yan jaridar su bada hakurin a jaridu takwas na kasa, baya ga biyan diyyar Naira biliyan 10.

leadership newspaper nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp