ƙasar Zanzibar za ta sassauta harajin da aka ƙara kan sukarin da ake shigarwa a kasar domin sauƙaƙa matsalolin kuɗi, duba da karatowar watan Ramadan.
Shugaban kasar, Hussein Ali Mwinyi, ya gargadi ‘yan kasuwa game da hauhawar farashin kayan abinci, inda ya danganta tashin farashin kayyayaki na baya-bayan nan da karancin sukari.
Duk da ƙoƙarin da gwamnati ke yi na magance hauhawar farashin kayayyaki, Shugaba Mwinyi, ya nuna rashin jin daɗinsa ga ’yan kasuwa marasa gaskiya, saboda yadda suke ci gaba da tsadar kayayyaki wanda ke shafar muhimman abubuwa kamar rogo da kifi da kayan lambu da kuma ‘ya’yan itatuwa a kasar.
Yayin da watan Ramadan ke gabatowa, al’ummar Musulmi masu rinjaye a kasar Zanzibar na neman sauki daga matsalolin tattalin arziki.


 

 
 