Tsohon ministan matasa da wasanni, Barista Solomon Dalung ya bayyana cewa za su fara zanga-zanga a yau Alhamis domin nuna fushinsu kan yadda ake tafiyar da lamurra a kasar, kuma ya ce za su yi yi ne a cikin lumana.
Dalung ya bayyana haka ne a tattaunawar da ya yi da BBC.
Solomon Dalung, wanda tsohon minista ne a lokacin gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa za su yi zanga-zangar ne saboda “wannan ne yaren da gwamnati ke ganewa kadai.”
‘Yan Najeriya, musammamn matasa sun dage kan gudanar da zanga-zangar da aka tsara farawa daga yau Alhamis duk da kokarin da hukumomin kasar suka yi na lallashin su.


