Masu zanga-zanga a Kenya sun lashi takobin komawa kan tituna a wani shiri na ci gaba da zangar nuna kin jinin karin haraji duk da cewa shugaba William Ruto ya janye shirin na sa.
Mista Ruto ya janye matakin ne bayan da masu zanga-zangar suka kutsa kai cikin ginin majalisar dokokin kasar a ranar Talata, lamarin da ya rikiɗe zuwa tashin hankalin da ya haifar da mutuwar samar da mutane 20.
Ya ce jama’ar Kenya, sun nuna karara cewa basu son wannan doka, don haka an yi watsi da ita. A cewar BBC.
Amurka ta yi yi na’am da janyewar, sai dai masu zanga zangar sun ce ko a jikinsu, don haka babu gudu ba ja da baya.