Ƴansanda a California sun yi wa masu zanga-zangar nuna goyon bayan ga Falasɗinawa barazanar su watse ko su kamasu.
A wajen makarantar ɗaliban sai ƙara taruwa suke domin ƙara jaddada goyon bayansu.
Zanga-zangar adawa da yaƙin da ake a Gaza na ƙara ƙamari a Amurka.
Wakiliyar BBC ta ce ɗaliban na ɗaga hannu suna furta cewa a dakatar da kai hare-hare a Rafah, a tsagaita wuta kuma a bai wa Falasɗinawa ƴancinsu.