Manyan jami’an tsaron kasar nan na tattaunawa kan halin tsaro da kasar take ciki, musamman tun bayan fara zanga-zanga.
A yayin taron, jami’an tsaron sun fara da cewa mutane sun karya ka’idar ‘yancin da kundin tsarin mulki ya ba su na gudanar da zanga-zanga ba tare da tashin hankali ba.
Sun ce sanin kowa ne an fitar da sanarwar wasu mutane na shirin yi wa zanga-zangar kutse.
A yayin zanga-zangar, mutane sun rika kiran a sauya musu gwamnati wanda hakan ya ci karo da kundin tsarin mulki, yayin da wasu kuma ke daga tutocin kasashen waje wanda wannan tamkar cin amanar kasa ne, kuma ba za a amince da hakan ba in ji jami’an tsaron.
suka ce, duk wanda ya karya dokar kasa zai girbi abin da ya shuka inji su.
Jami’an tsaron sun ce a yayin zanga-zangar sun kama wadanda suka yi amfani da zanga-zanga suka yi fashi da sauran laifuka.
An soma zanga-zangar ce tun a ranar Alhamis din makon jiya, inda ‘yan Najeriya ke neman gwamnati ta samar musu da sassaucin wahalhalun rayuwa da suke ciki, abin da ya haifar da kone-kone da rasa rayukan jama’a, baya ga haifar da gibi ga tattalin arziki.
An tsara gudanar da zanga-zangar ce a tsawon kwana goma, daga 1 zuwa 10 ga watan Agustan 2024.