fidelitybank

Zancen daukar mutane aikin soja bogi ne da zamba cikin aminci – Rundunar Soji

Date:

Rundunar Sojan Najeriya ta gargadi jama’a kan daukar ma’aikata ta kafar internet na bogi da ake yadawa a shafukan sada zumunta da sauran kafafen sadarwa cewa, zamba ne kawai tsagwaranta da ake tallata daukar ma’aikata zuwa NA 83 Regular Recruit Intake.

Rundunar a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, ta ce, shafin daukar ma’aikata na da nufin damfarar ‘yan Najeriya.

Hanyar hanyar shafin internet din shine: https://recruitment.army.mil.ng/darrr wanda kawai ya kasance na karya ne.

Sanarwar ta kara da cewa: “Wannan ci gaban da bai dace ba, NA na son sanar da jama’a karara cewa, babu wani daukar ma’aikata da ake ci gaba da yi, kamar yadda aka buga a kafar yada labaran karya. Bayanin karya ne, yaudara da nufin damfarar jama’a wadanda ba su ji ba gani.

“Saboda haka, an umurci jama’a da su yi hattara da dillalan daukar ma’aikata na karya ta yanar gizo wadanda ke matukar farautar wadanda abin ya shafa.”

Rundunar ta lura cewa, ana buga tallace-tallacen daukar ma’aikata da Sojoji ke yi a jaridun kasar nan.

vgn news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp