Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas, ya yi barazanar cewa zai yi yaki domin ganin ya gama aiki da tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Prince Uche Secondus.
Secondus dai na hannun damar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar.
Wike ya yi wannan barazanar ne a ranar Asabar din da ta gabata a wajen bikin kaddamar da gina titunan cikin garin Omagwa da ke karamar hukumar Ikwerre a jihar Ribas.
Gwamnan ya ci gaba da cewa zai “gama” duk wanda ya kafa tantinsa da “makiya jihar”.
Ya ce, “Idan wani ya yaki tsarinmu, za mu yaki mutumin.
“Bari in gaya muku abin da ba ku fahimta ba a siyasa. A duk lokacin da kuka ce kuna aiki tare da mu kuma gobe kuka koma ga makiyinmu, za mu dauki dukkan karfin da muke da shi, har ma za mu bar makiyinmu mu gama da ku tukuna.
“Don haka dukkan ku da za ku koma Abuja domin yin taro da makiyanmu a jihar, zan karasa ku zuwa karshe.
“Mun tsige Shugaban Jam’iyyar na Kasa wanda bai yi kyau ba. Dukkansu suna nan, duk mun amince, yanzu za su je Abuja su yi taro da mutumin da muka cire, a tunanin za ku yi amfani da wannan wajen yakar mu, mu murkushe su”.


