Babban kocin Flying Eagles, Ladan Bosso, zai yi amfani da damarsa wajen rage ‘yan wasansa, da suka kas ta ka rawa a wajen horon kungiyar.
A yau litinin ne tawagar ta koma sansani, domin tunkarar gasar cin kofin nahiyar Afirka na ‘yan kasa da shekaru 20 na shekarar 2023 a Abuja.
‘Yan wasa 35 a halin yanzu suna fafutukar neman gurbi a kungiyar.
Ana sa ran kwararrun da aka gayyata daga kasashen waje za su hada kai da takwarorinsu a sansanin mako mai zuwa.
Ana sa ran Bosso zai mika jerin sunayen ‘yan wasa 21 na karshe a gasar a ranar 20 ga watan Janairu.
Tawagar za ta fara rangadin atisaye a Morocco a karshen wannan watan.
Flying Eagles za ta kara da Masar da Mozambique da Senegal a rukunin A a gasar ‘yan kasa da shekaru 20 ta 2023.