Jigo a babbar jam’iyyar hamayya ta PDP a Najeriya ya ce zai bai wa shirin hadakar ‘yan hamayya cikakken haɗin kai da goyon baya don tabbatar da cewa an kawar da jam’iyyar APC a babban zaɓen 2027.
Sule Lamido, ya ce yana cikin jam’iyyar PDP daram amma zai yi wa jam’iyyar ADC aiki kamar yadda Nyesom Wike, ya ke yiwa jam’iyyar APC aiki alhali kuma ɗan PDP ne.
Tsohon gwamnan na Jigawa ya ce akwai rainin hankali dangane da yadda ake tafiyar da harkokin siyasa da abin da Wike ya ke musu a PDP, don haka shi ma dole ya marawa ADC kuma babu wanda zai rabashi da PDP.
Sule ya nuna cewa halin da Najeriya ke ciki a yanzu ba lokaci ba ne na nuna ɓangaranci ba, lokaci ne na duba wane ne ya cancanta a mara masa baya ba tare da la’akari da jam’iyya ba.
Ya ce batun Jam’iyya ya haifar da tarin kalubale da matsaloli na ɓangaranci da rabuwar kawuna a Najeriya wanda dole ne a warware hakan.
Ya ce duk matsalolin PDP haddasata aka yi, don haka babu inda zai je, kuma babu wanda ya ke tsoro ko nuna munafurci.
Ya ce abubuwa da dama ana sa son zuciya a ciki, don haka shi ya san tsarin da zai bi saboda al’umma ce a gabansa. Kuma dole ya yi aiki domin kare PDP da bai wa ADC ƙasar.