fidelitybank

Zan yi titina da da gadar sama a Edo – Sabon Gwamna

Date:

Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebolo a ranar Talata ya yi alkawarin yin hadin gwiwa da gwamnatin tarayya, kamfanoni masu zaman kansu, kungiyoyi masu zaman kansu, wadanda ke kasashen waje, da sauran masu ruwa da tsaki, domin bunkasa dukkanin sassan tattalin arzikin jihar.

Okpebholo ya yi wannan alkawarin ne a jawabinsa na farko jim kadan bayan rantsar da shi a matsayin gwamnan jihar.

Sabon Gwamnan da aka rantsar wanda ya yi nuni da cewa, halin da tituna ke ciki ya sanya jama’a ke da wahala wajen kaura daga wannan yanki zuwa wancan, ya yi alkawarin cewa nan da nan gwamnatinsa za ta fara aiki don ganin an sake bi hanyoyin.

Ya kara da cewa, wani bangare na ajandarsa shi ne, samar da ababen more rayuwa, da gina magudanan ruwa da gadoji, domin saukaka harkokin sufuri ga kowa da kowa.

Ya kuma yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta tallafa wa masu kananan sana’o’i da kuma mata masu kasuwa da rance mai sauki.

Ya kuma bayyana shirin gwamnatin sa na daukar malamai da sake gina ajujuwan da ba su da kyau a fadin jihar.

“Gwamnatina za ta gaggauta daukar matakin daukar malamai da sake gina ajujuwan da suka lalace. Za a kuma karfafa ilimin manyan makarantu ta hanyoyi da dama, don tabbatar da ingantaccen ilimi.

“Ba za a bar mu da yawan matasan mu ba. Za mu tallafa musu don samun dabarun da suka dace don karfafa kansu,” in ji shi.

Ya ce gwamnatinsa a shirye ta ke ta hada al’ummomin da har yanzu ba a hada su da wutar lantarki ta kasa ba, don tabbatar da sun samu wutar lantarki.

nigerian news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp