fidelitybank

Zan yi mulkin gaskiya da ƙanƙastar da kai – Matashin shugaban kasar Senegal

Date:

Zaɓaɓɓen shugaban Senegal Bassiorou Diomaye ya yi alƙawarin yin mulki tare da ƙanƙastar da kai da kuma nuna gaskiya.

Ya bayyana haka ne a jawabinsa na farko bayan zaɓen shugaban ƙasar da aka yi ranar Lahadi.

Babban abokin hamayyar Mista Faye daga jam’iyya mai mulki Amadou Ba tuni ya amince da shan kaye abin da ya sa Faye mai shekara 44 ya zama shugaban ƙasa mafi ƙanƙantar shekaru a tarihin ƙasar.

“Zaɓe na da aka yi ya nuna al’ummar Senegal sun amince su tsame kansu daga abubuwan da suka faru a baya,” kamar yadda ya faɗa wa ƴan jarida a ranar Litinin.

“Na yi alƙawarin yin shugabanci tare da ƙanƙan da kai da kuma gaskiya.”

Ɗaya daga cikin manyan ƙudurorinsa a matsayin shugaban ƙasa shi ne “haɗa kan ƴan kasa” sakamakon yadda aka shafe shekara uku ana tashin hankali da kuma rikicin siyasa a ƙasar, kamar yadda Mista Faye ya bayyana. In ji BBC.

Ya kuma yi alƙawarin “yaƙar cin hanci a kowane mataki” da sake gina hukumomi tare da magance matsalar tsadar rayuwa.

Mista Faye ya kuma gode wa shugaba Macky Sall mai barin gado ganin yadda ya taimaka aka gudanar da zaɓe cikin cikin nasara.

Sakamakon zaɓen wanda ba na hukuma ba ya nuna Mista Faye ne ke kan gaba da kusan kashi 53.7 cikin 100 yayin da Mista Ba yake da kashi 36.2 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa.

Nasararsa na zuwa ne ƙasa da mako biyu bayan da aka sake shi daga gidan yari.

nnn.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuƙa...

Kallo Ya Koma Sama: Elon Musk zai fuskanci mummunar sakamako – Trump

Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka...

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...
X whatsapp