fidelitybank

Zan yi ban kwana da PDP kafin ƙarshen watan Maris – Kwankwaso

Date:

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jigo a jam’iyyar PDP mai hamayya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce, zai fice daga jam’iyyar kafin karshen wannan watan na Maris.

Tsohon gwamnan ne ya tabbatar wa BBC Hausa wannan labari, inda ya ce, ya yi nisa a shirinsa na komawa jam’iyyar NNPP watau New Nigeria Peoples Party.

Wani makusancin tsohon gwamnan ya ce babu tsari a game da yadda ake tafiyar da sha’anin jam’iyyar ta PDP, lamarin da ya tilasta wa Sanata Kwankwaso tattara kayansa domin ya fice daga cikinta.

A watan jiya ne Kwankwaso ya jagoranci wani gagarumin taro na wasu manyan siyasar kasar karkashin wata kungiya mai suna The National Movement TNM.

A baya dai, Sanata Kwankwaso ya nuna rashin jin dadinsa game da yadda jam’iyyar PDP take kokarin mayar da shi dan bora duk da gudunmawar da yake bayarwa a cikin jam’iyyar.

An dade ana kai ruwa rana tsakani tsohon gwamnan na Kano da bangaren tsohon ministan harkokin waje, Aminu Wali.

Kwankwaso ya koma jam’iyyar PDP ne daga jam’iyyar APC bayan zaben 2015, sakamakon takun-sakar da aka rika yi tsakaninsa da wanda ya gaje shi, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

A shekarar 2019, ya tsayar da tsohon Kwamishina a gwamnatinsa, Abba Kabir Yusuf a matsayin dan takarar jam’iyyar PDP na gwamnan jihar ta Kano, ko da yake ya sha kaye a hannun Gwamna Ganduje.

tribune

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp