Sarkin jihar Katsina, Abdulmumin Kabir, ya ce, ba zai yiwu dan takarar shugaban kasa na jamâiyyar PDP, Atiku Abubakar ya lashe zaben shugaban kasa a 2023 ba.
Dakta Kabir ya bayyana haka ne a lokacin da kungiyar yakin neman zaben Atiku ta kai masa ziyara a fadarsa da ke Katsina a ranar Talata
Sarkin Katsina a lokacin da yake nuna bakin cikinsa kan halin da kasar nan ke ciki, ya ce zai yi adduâa ne kawai ga âyan takarar da suke shirye don magance matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a kasar.
Ya godewa Atiku kan yadda ya bayyana aniyarsa ta magance munanan matsalolin rashin tsaro da talauci a kasar nan idan har aka zabe shi shugaban kasa a 2023.
Daga cikin tawagar Atiku zuwa Katsina domin gudanar da gangamin akwai mataimakinsa kuma gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Iyorchia Ayu da sauran tsaffin gwamnoni da sanatoci da dai sauransu.