fidelitybank

Zan tallafawa Kano wajen magance matsalar tattalin arziki – Ɗangote

Date:

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya alƙawarta tallafa wa tsare-tsaren manunfofin taimaka wa al’umma da ci gabansu, domin magance matsalolin tattalin arziki a jihar Kano.

Dangote ya yi wanna alƙawarin ne a lokacin da ziyarci gwamnan jihar Kano Abba Yusuf a gidan gwamnatin jihar ranar Juma’a.

Cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ya ce Dangote ya ce yana sane da halin matsin rayuwa da talakawan ƙasar ke fuskanta.

Dangote ya alƙwarta bayar da tallafi don inganta fannonin lafiya da ilimi da hanyoyin yaƙi da talauci ga masu ƙaramin ƙarfi a jihar.

Attajirin ɗan kasuwar ya alƙawarta yin aiki kafaɗa dakafaɗa da gwamnatin jihar don bunƙasa ci gaban al’ummar jihar.

A nasa ɓangare gwamnan jihar ya gode wa hamshaƙin ɗan kasuwar bisa manyan ayyukan ci gaba da ya samar musamman sashen kula da masu buƙatar gaggawa da ɗakunan tiyata da na haihuwa da na yara a asibitin Murtala da ke jijar.

Sannan kuma gwamnan ya buƙacin Dangote ya tallafa wa jihar don gina tashar samar da wutar lantarki mai zaman kanta domin farfaɗo da masana’antun jihar don bunƙasa har tattalin arziki da kuma ƙarffa jihar.

Haka kuma Gwamna Abba Kabir ya shaida wa Dangoten cewa jihar na cikin tsananin buƙatar asibitin kula da masu lalalar cutar sikila domin samar da magunguna kyauta ga masu lalurar.

A ɓangaren ababen more rayuwa, gwamnan jihar ya buƙaci tallafin Dangote don gina tituna na zamani, da gidaje, da ci gaban al’umma da sauran fannoni.

vgn news today 2021

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp