Majalisar dokokin jihar Rivers ta zaɓi Edison Ehie a matsayin kakakinta.
Zaɓen nasa ya gudana ne a yayin zaman majalisar, inda ‘yan majalisar 26 suka kada kuri’ar amincewa da shi.
Wannan hukuncin ya biyo bayan dakatarwar da aka yi wa wasu manyan shugabannin majalisar.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa bayyanar Ehie a matsayin sabon shugaban majalisar ya biyo bayan da ‘yan majalisar guda 26 suka tsige magabacinsa, Martins Amaehule,
Da yake zantawa da manema labarai bayan zaben sa, Ehie ya bayyana jin daɗinsa ga abokan aikinsa da suka ɗora masa alhakin jagorantar majalisar.
“Alƙawarina ga mutanen Rivers shine zan kasance mai adalci ga kowa da kowa; Zan tabbatar da bin doka da oda.
“Ba zan ci amanar abokan aikina ba. Ba zan ci amanar mutanen Rivers ba. Ba zan ci amanar mazaba ta ba.”
“Zan tabbatar da ‘yancin cin gashin kan Majalisar Dokokin Jihar Ribas, tare da mutunta juna ga bangaren shari’a da bangaren zartarwa na gwamnati,” inji shi.
Bugu da kari, sabon kakakin ya bayyana cewa zai tabbatar da cewa ‘yan majalisar da aka dakatar sun samu sahihin saurare ta hanyar kwamitin koke.