Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi barazanar korar duk ministan da bai taɓuka abin kirki a ma’aikatarsa ba.
Tinubu na wannan maganar ne a lokacin taron bitar kwana uku da aka shirya wa ministoci mataimaka na musamman ga shugaban ƙasar, da manyan sakatarorin gwamnati, da sauran manyan jami’an gwamnati .
Shugaban ƙasar ya ce ya zaɓo manyan jami’an gwamnatin nasa ne domin su taimaka a ci nasarar tafiyar da gwamnati tare.
Ya ƙara da cewa “a ƙarshen wannan bita, za mu sanya hannu a kan takardar yarjejeniyar fayyace ƙwazon aiki”.
“Don haka ne ma muka ɓullo da sashen tantance ƙwazo, kuma a ƙarshen wannan bita za ku saka hannu kan yarjejeniyar fahimta tsakaninku (ministoci) da manyan sakatarorin gwamnati da kuma ni kaina”, in ji Tinubu.
“Matuƙar ka yi ƙwazo, babu abin fargaba a ciki, idan kuwa ba ka yi komai ba, za mu duba, matuƙar babu abin da ka yi, za mu sauke ka, babu wanda zai iya rayuwa shi kaɗai”.