Mamallakin kamfanin Twitter Elon Musk ya ce yana duba yiwuwar sauya wa shafin sabon tambari.
Cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Elon Musk ya ce ”Nan ba da jimawa ba za mu sauya wa twitter tambari, ta hanyar musanya hoton tsuntsun da a yanzu ke mazaunin alamar shafin.
Ya ƙara da cewa za a sauya hoton tsuntun da alamar harafin ‘X’
Hamshaƙin ɗan kasuwar ya ce ya zaɓi sauya wa shafin tambarin ne domin tabbatar da shafin ya bambanta da kowanne.
Elon Musk ya kuma bayar da samfurin misalin yadda sabon tambarin shafin za ta kasance, ta hanyar wallafa bidiyon sabon tambarin a shafinsa.
A baya-bayan nan dai mai kamfanin Meta da ya mallakin shafin Facebook da Instagram da Whatsapp ya kaddamar da sabon shafin ‘Thread’ da ake kallo a matsayin kishiya ga shafi Twitter.
Shafin da ya samu miliyoyin mabiya a faɗin duniya