Watanni biyar bayan da aka yankewa malamin makarantar nan Abdulmalik Tanko, hukuncin kisa, bisa samunsa da laifin kashe daliba Hanifa Abubakar mai shekaru biyar, tuni dai Gwamna Abba Yusuf, ya sha alwashin ganin an zartar da hukuncin kisa ga wanda ake tuhuma.
Gwamnan ya ce, dole ne a aiwatar da hukuncin da kotu ta yanke.
Abba Kabir Yusuf ya bayyana haka ne a yayin wani taron tunawa da ranar yara ta duniya ta 2024 a Kano.
Wata babbar kotun jihar Kano ta yanke wa Abdulmalik Tanko da wanda ake zargin Hashimu Ishyaku hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan ta same su da laifin kisan Hanifa.
Gwamnan ya ce, tabbatar da cewa, wadanda aka yankewa hukuncin kisa sun gurbi abun da suka shuka, ta hanyar ne kadai zai zama izina ga masu neman aikata irin wannan laifin.
A cewarsa, jihar na gab da ayyana dokar ta baci kan ilimi domin tabbatar da ingantaccen ilimi ga yara a Kano.
Gwamnan ya kuma yi alkawarin cewa, nan da wani lokaci, za a fara ciyarwa a makarantu kyauta da kuma bayar da tufafi kyauta ga yara ‘yan makaranta daga ajin firamare na daya har zuwa aji.