fidelitybank

Zan ruguza PDP da ‘yan cikinta – Dan PDP a jawabin taron nnpp

Date:

Wani jigo a jam’iyyar PDP a karamar hukumar Warri ta Kudu a jihar Delta, Victor Umukoro ya ce, shi da wasu irinsa za su ruguza jam’iyyar tare da sake gina ta domin inganta Nijeriya.

Ya yi wannan jawabi ne ga dan takarar Sanatan Delta ta Kudu na jam’iyyar New Nigerian People’s Party, NNPP, Omatseye Nesiama a wani taro na gari da NNPP ta shirya a Warri.

Ya ce, “Ni dan PDP ne. Ni dan PDP ne abin da na fada ya isa haka. Zamu ruguza wannan PDP, mu sake gina PDP domin sabuwar Najeriya.

Tsohon dan takarar shugabancin karamar hukumar Warri ta Kudu ya ce wasu ‘yan jam’iyyar sun fusata saboda kazantar siyasar da ake zargin ana tafkawa a jam’iyyar.

“Suna ce maka Oga ya gama magana. Tsarin yayi magana. Mun gaji. Za mu kawo karshensa.”

Umukoro ta ce mutane irin su Omatseye Nesiama ne wadanda suka samu horo sosai kuma sun yi balaguro da su ke bukata a matsayinsu na wakilai.

“A dalilin zaben nan, ni ba dan jam’iyya ba ne. Ni mai kallo ne.”

Karanta Wannan: Shugaban PDP a Yobe ya koma APC

Umukoro, ya yi korafin cewa suna da koma-baya a siyasance a tsarin Essi da ke Warri, tare da yin kira ga al’ummar yankin da kada su ji tsoron duk wata barazana a lokacin zabe mai zuwa amma su fito baki daya su zabi Omatseye Nesiama.

Tun da farko, Omatseye Nesiama ya tabbatar da cewa har yanzu yana nan a takarar kuma babu gudu babu ja da baya, yana mai shan alwashin cewa a shirye yake ya yi aiki tare da kawo sauyi a majalisar dattawa.

legit.ng.news.

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp