fidelitybank

Zan rufe duk wani banki da ya bijirewa umarnin CBN – Soludo

Date:

Gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo, ya umarci mazauna jihar da su ci gaba da amfani da tsofaffin takardun naira 200 da 500 da 1,000 tare da sababbin takardun kuɗin a ko’ina cikin jihar.

Cikin wata sanarwa ta musamman da Charles Soludo wanda tsohon gwamnan babban banki ne, ya ce, babban bankin ƙasa ya umarci bankunan kasuwanci a ƙasar da su ci gaba da biyan masu ajiyar kuɗi a bankunan da tsofaffin takardun kuɗi.

Sannan kuma su ci gaba da karɓar tsofaffin takardun kuɗin a duk lokacin da aka gabatar da su.

Karanta Wannan: Sai na kulle duk wani banki da kantin da ya ki karbar tsofaffin kudi – Gwamnan Ogun

Gwamnan jihar ta Anambra ya ce, ya tabbatar da sahihancin umarnin yayin wata hira da ya yi da gwamnan babban bankin Godwin Emefiele ta wayar tarho a ranar lahadi da daddare.

Soludo ya ce, gwamnan CBN ya bayar da wannan umarnin ne yayin wani taro da babban bankin ya yi da bankunan ƙasar da aka yi a ranar Lahadi 12 ga watan Maris.

Gwamnan na Anambra ya kuma buƙaci al’ummar jihar da su kai ƙarar dukkan bankin da ya ƙi bin umarnin babban bankin na biya da karɓar tsofaffin takardun kuɗin.

Ya na gargaɗin cewa gwamnatinsa za ta rufe duk bankin da ya bijire wa wannan umarnin.

A ranar 3 ga watan Maris ne kotun ƙolin Najeriya ya yanke hukuncin ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kuɗin ƙasar har zuwa 31 ga watan Disamban 2023.

Wasu jihohin kasar ne dai suka shigar da ƙara a gaban kotun, suna neman a ɗage wa’adin da CBN ya sanya na daina amfani tsofaffin kuɗin.

national tribune newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp