Kocin Super Eagles, Jose Peseiro, ya ce a shirye yake ya amince da rage albashinsa domin ya ci gaba da horas da Najeriya.
A halin yanzu dan kasar Portugal din yana karbar dala 70,000 duk wata kan kwantiraginsa da zai kare a watan Yuni.
Har yanzu dai Peseiro bai cimma matsaya ba da hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF, lamarin da ya sa ake tunanin za a dauki wani koci.
Vanguard ta ruwaito cewa, hukumar NFF karkashin jagorancin Ibrahim Gusau na kokawa kan yadda Peseiro ke biyan albashi mai tsoka, wanda hukumar Amaju Pinnick ta sasanta.
Da farko, an yi imanin cewa fadar shugaban kasa za ta biya albashin mai kula da Eagles. Amma abin ba haka ya kasance ba, ana bin kocin bashin watanni shida.
Wani zabin da hukumar NFF ke da shi shi ne, idan Peseiro ya amince a rage masa albashi, hakan zai samar da ma’auni ga duk wanda ya amince ya fara aikin a nan gaba.