fidelitybank

Zan nesanta kai na da Abuja da zarar na sauka – Buhari

Date:

Shugaba Muhammadu Buhari, ya ce, zai koma mahaifarsa Daura da ke jihar Katsina, idan ya miƙa ragamar mulki ga sabuwar gwamnati mai zuwa a ranar 29 ga watan Mayu.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Femi Adesina ya fitar, ya ce, Buhari ya faɗi haka ne jiya Laraba lokacin da ya karɓi bakuncin Jakadiyar Birtaniya a Najeriya mai barin gado, Catriona Wendy Laing.

Buhari ya yaba wa ƙasar Birtaniya kan tallafa wa Najeriya a ɓangarori da dama, musamman ma wajen sake gina yankin arewa maso gabas da ayyukan ƴan tayar da ƙayar-baya ya ɗaiɗaita.

Ya ce Birtaniya ta kasance gida ga ƴan Najeriya da dama, inda ya ce dangataƙar ƙasashen biyu za ta ci gaba da wanzuwa.

Tun da farko, Jakadiyar Birtaniyar ta ce ba ta jin daɗi barin Najeriya da za ta yi, musamman ma ganin cewa ta saba da abubuwa da dama a ƙasar, kamar al’adu da raye-raye da kuma wakokin ƴan ƙasar masu daɗi.

Ta ce ta ji daɗin kasancewarta a Najeriya, inda ta ce ta ziyarci jihohi sama da 20. Ta ce “na faɗa wa wanda zai gaje ni da shi ma idan ya zo ya rika yin irin abubuwan da na yi.

assu update

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp