fidelitybank

Zan maye gurbin Ancelotti idan Madrid ta siyo min dan wasa na – Zidane

Date:

Kocin Faransa, Zinedine Zidane ya baiwa shugaban Real Madrid Florentino Perez sharadi daya da zai cika kafin (Zidane) ya dawo a matsayin kocin kungiyar.

Bafaranshen na son komawa Santiago Bernabeu ne kawai idan Perez ya amince ya sayi Rayan Cherki, in ji Sport.

Tsohon dan wasan Real Madrid kuma kocin yana sha’awar yin aiki tare da dan wasan Faransa.

An ce Zidane ya shaidawa Perez cewa zai koma kungiyar a matsayin wanda zai maye gurbin Carlo Ancelotti idan har ya samu tabbacin siyan Rayan Cherki.

Ana dai kallon Cherki a matsayin daya daga cikin matasan ‘yan wasa mafi burgewa a fagen kwallon kafa a Turai a halin yanzu kuma Zidane ya kasance babban masoyin dan wasan gaba.

Makomar Ancelotti a kungiyar ta Sipaniya ba ta da tabbas, duk da tsohon kocin da ya jagoranci Los Blancos a gasar La Liga da gasar zakarun Turai a bara.

Real Madrid ce ta biyu a teburin gasar da maki takwas tsakaninta da abokiyar hamayyarta Barcelona.

daily sun news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp