fidelitybank

Zan mayar da hankali bangaren noma da ma’adanai a Zamfara – Tinubu

Date:

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress, APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya tabbatarwa ‘yan asalin jihar Zamfara cewa, zai mayar da hankali kan harkar noma da ma’adanai, domin bunkasa tattalin arzikin jihar idan aka zabe shi a zabe mai zuwa.

A cewarsa, ci gaban sassan gaba daya zai samar da karin guraben ayyukan yi da za su iya rage yawaitar aikata miyagun laifuka a jihar.

Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin yakin neman zabensa a harabar baje kolin kasuwanci da ke Gusau, babban birnin jihar, inda ya ce duk da wannan zagon kasa, APC za ta gudu da nasara a duk zabe.

Ya ci gaba da cewa, ba ya je jihar Zamfara domin yakin neman zabe, sai dai ya yi godiya ga jama’a saboda dimbin goyon bayan da suke ba jam’iyyar tun bayan da Nijeriya ta dawo mulkin dimokuradiyya a hannun sojoji a 1999.

A cewarsa, jihar Zamfara ta samu albarkatun mutane da na kasa wadanda ke bukatar ci gaba domin bunkasa tattalin arzikin kasa da jihar baki daya.

Ya yabawa Gwamna Matawalle da tsohon Gwamna Ahmad Sani Yarima da tsohon Gwamna Aliyu Mahamud Shinkafi da tsohon Gwamna Abdul Aziz Yari bisa gudunmawar da suka bayar wajen ganin APC ta kasance karkashin inuwa daya a jihar.

“Har yanzu zan dawo jihar Zamfara domin yin biki na musamman idan lokaci ya yi,” in ji shi.

nigerian news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp