fidelitybank

Zan marawa gwamnatin APC baya a Ekiti – Fayose

Date:

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya sha alwashin marawa zababben gwamnan jihar, Biodun Oyebanji baya domin ci gaban jihar Ekiti.

Wannan dai na zuwa ne a daidai ranar da ya mayar da goyon bayansa na tsayawa takarar shugabancin kasa a kudancin kasar duk da cewa, jam’iyyarsa ta PDP ta gabatar da dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar wanda ya fito daga yankin Arewa.

Rahotanni sun bayyana cewa, tsohon gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake karbar bakuncin Oyebanji, wanda ya kai masa ziyara, bayan lashe zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Yuni a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress.

Kalaman Fayose: “Na yi alkawari zan goyi bayan gwamnatin Oyebanji a kowane fanni da za a bukaci goyon bayansa. Ci gaban jihar Ekiti kokari ne na hadin gwiwa.

“Dole ne ku kalli duk mutanen Ekiti a matsayin naku. Kai ne gwamnan kowa ba tare da la’akari da siyasa ba”.

A halin da ake ciki, Oyebanji ya ce, ya kai ziyarar ne domin mika gaisuwa ga Fayose a matsayinsa na tsohon gwamnan jihar, wanda a cewarsa, ya nuna kishin kasa ta hanyar taya shi murna jim kadan bayan bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 18 ga watan Yuni.

kano news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp