fidelitybank

Zan kori duk ma’aikacin da bai dawo daga yajin aiki ba nan da awa 72 – Gwamnan Ebonyi

Date:

Gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, ya yi barazanar sallamar duk wani ma’aikacin da ya shiga yajin aiki nan da awa 72 idan bai koma aiki ba.

 

Gwamna Nwifuru ya bayyana haka ne a ranar Litinin a ofishinsa da ke Abakaliki a lokacin da yake jawabi a game da yajin aikin da shugaban ƙungiyar ƙwadago na jihar, Kwamrade Comrade Oguguo Egwu ya fitar, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

 

A ranar Lahadi ne Oguguo ya bayyana cewa yajin aikin biyayya ce ga umarnin shugaban ƙungiyar na ƙasa na ranar 8 ga Nuwamban 2024, inda ta yi kira ga ma’aikata a duk jihar da ba a fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi ba su shiga yajin aiki.

 

Nwifuru, ya ce majalisar tarayya ba ta ƙayyyade sabon albashi ba, inda a cewarsa dokar ta yi magana ne kan mafi ƙarancin albashi.

 

“Na fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi tun a watan Oktoba, shi ya sa na yi mamaki da na ga sun fara yajin aiki. Kuma babu wani ma’aikaci da yake binmu bashin albashi, haka ma ƴan fansho.

 

“Don haka duk wanda bai koma aiki ba nan da awa 72, zan sallame shi, in ɗauki wasu.

 

Gwamnan ya ƙara da cewa ya bayar da umarnin a fara ɗaukar sunayen waɗanda suke zuwa aiki, sannan ya ce babu maganar zaman sulhu, “saboda kwamrade Egwu ba ma’aikacinmu ba ne.”

legitnews.ng

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp