Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce, zai je Qatar domin tattaunawa kan sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙin da ake yi tsakanin Hamas da Isra’ila.
Macron ya bayyana haka ne a yayin taron sauyin yanayi na Majalisar Ɗinkin Duniya da ake kira “Cup28” wanda yake gudana a Dubai.
A jiya Isra’ila ta ci gaba da kai hare harenta a Zirin Gaza bayan tsagaita wuta da aka yi ta kwanaki 7.
Ma’aikatar lafiya a Gaza ta ce an kashe ƙarin Falasɗinawa 193 tun lokacin da Isra’ila ta ci gaba da kai hare-hare a Zirin Gaza ranar Juma’a.
Ta ce an kuma raunata wasu mutum 652 tun bayan ƙarewar wa’adin tsagaita wuta na kwana bakwai.
A cewar hukumomin lafiya na Hamas, adadin mutanen da aka kashe a Gaza ya zarce 150,000 kuma kashi 70 daga cikinsu mata ne da ƙananan yara.


