Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara, ya karɓi wata dattijuwa wadda ƴan bindiga suka sace da kuma bidiyonta ya karaɗe shafukan sada zumunta.
Bidiyon dai ya nuna wata uwa da ‘ya’yanta a hannun ƴan bindiga, waɗanda har suka koma cin ciyawa. Sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar, na cewa ganin halin da matar ta shiga, ya zama tilas a tashi haikan wajen shawo kan matsalar ta ƴan fashin daji da kuma tabbatar da cewa iyalai sun samu ababen more rayuwa.
Sanarwar ta ce gwamnan ya karɓi matar ne domin hakan na cikin zimmarsa ta ganin an kare rayuka da ma dukiyoyin al’ummar Zamfara.
“Gwamna Lawal ya karɓi Hauwa’u Salisu, matar da ta rasa komai saboda rikicin ƴan fashin daji.
Ya nuna zimmarsa ta ganin an kawo karshen matsalar tsaro a Zamfara, sannan ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan da ayyukan ƴan bindiga ya daidaita,” in ji sanarwar.
Gwamnan ya bai wa matar wani sabon gida da za ta zauna da ‘ya’yanta. Ya kuma tabbatar wa matar cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ciyar da ‘ya’yanta da kuma samar musu abubuwan da suke buƙata.
Har ila yau, gwamnan ya bayar da umarnin cewa a gaggauta sanya yaran matar a makaranta da kuma ba su cikakken tallafin karatu.
Ya kuma buƙaci dukkan hukumomi su yi ƙoƙari wajen binciko iyalai marasa galihu da ke fuskantar irin waɗannan matsaloli, don ganin cewa an ba su taimakon da ya kamata